Duniyar Earth


Hoton duniyar Earth 

Duniyar Earth itace duniya ta uku dake kusa da rana, kawo yanzu ita kadai ce duniyar da abu mai rai ya tabbata a cikinta. Masana ilimin sararin samaniya sun dukufa shekara da shekaru wajen binciko wata duniya wadda za a iya samun halitta mai rai amma har yanzu abin yaci tura. 

Duniyar Earth itace duniyar da dan Adam da sauran dukkan halittu masu rai ke rayuwa. A duk cikin duniyoyin da Allah ya halitta babu kamar Earth saboda ita kadai ce ta Æ™unshi muhimman sinadaran rayuwa guda biyu wato ruwa da oxygen  — Cikin kashi 71% na duniyar Earth ruwa ne ya mamayeta na daga tekuna da manyan rafuka, sai kuma sinadarin oxygen kashi 21% wanda itatuwa da tsirrai ke samarwa, Nitrogen kuma 78%, sinadarin argon kuma 0.93% sai sinadarin carbon dioxide 0.04%.

Duniyar Earth itace ta biyar a girma daga cikin gungun duniyoyin dake cikin falaki. Amma bata kai girman manyan duniyoyi masu kunshe da iskar gas ba irin su  — Jupiter, Uranus Saturn da Neptune amma ta dara duniyoyin duwatsu guda uku irin su  — Mercury, Mars da Venus.

Yadda duniyoyi ke tafiya a falakinsu suna zagaye rana

Kamar yadda duniyoyi suke zagaye rana itama haka duniyar Earth tana zagaye rana a bisa falakinta daga kusurwar kudu zuwa kusurwar arewa (South Pole and North Pole). Tana daukar awoyi 23.934 kafin ta gama kewaye daya na falaki (axis) wato shine kwana daya, tana kuma daukar kwanaki 365.26 kafin ta gama zagaye daukacin da'irar shataletalen falaki (Orbit) wato shekara guda kenan cif.

Daga cikin duniyoyin falaki kaf wacce tafi kama da duniyar Earth itace duniyar Mars ta ƙunshi abubuwa masu kamanceceniya da ita sosai, amma ga bayanai nan daki-daki game da wannan jar duniya.

Duniyar Mars


Hoton duniyar Mars wacce ake wa lakabi da Jar duniya

Duniyar Mars ita ce duniya ta huÉ—u  da ke kusa da rana bayan duniyar É—an Adam daga cikin duniyoyi tara kamar yadda masana ilimin  sararin samaniya suka bayyana. Kuma wannan suna nata ya samo asali ne daga  wani gunkin Romawa. Gaskiyar ita ce Romawan sun kwaikwayi mutanen Girka na zamanin baya waÉ—anda suka saka wa duniyar ta Mars sunan ubangijin yaÆ™insu wato Ares, Sauran al'ummomi na mutanen farko su ma sun bai wa duniyar suna dangane da launin ta - Misali, mutanen Masar sun saka wa duniyar Mars suna "Her Desher," ma'ana "Ja," haka su ma Æ´an sama jannti na Æ™asar China na wancan lokacin sun mata laÆ™abi da "tauraruwa mai wuta."  Haka kuma baki É—aya girman duniyar  Mars bai fi rabin girman duniyar da mutane ke zaune a ciki ba! sai dai kuma cike take da duwatsu da kwazazzabai waÉ—anda suka kera wanda ake dasu a duniyar É—an Adam.

To har'ila yau kuma kwana ɗaya a duniyar Mars ya fi na duniyar ɗan Adam da awa 12. Wato kamar yadda kowa yasan cewa awa 24 suke kwana ɗaya a duniyarmu, ita duniyar Mars awa 36 kenan ke kwana ɗaya. Hakan ne kuma yasa kwanaki 687 ne ke shekara guda a Mars, saɓanin kwanaki 365 a duniyar dan Adam.

Ikon Allah ba shi da iyaka, domin kuwa har'ila yau duniyar Mars  da akwai kwazazzabai da dama masu yanayi da wutsiyar koguna to sai dai a Æ™afe suke sabo da tsananin sanyi wanda ke sa duk wani abu mai ruwa-ruwa na wurin ya sandare.

To mai yiwuwa mutum ya yi tunaniq cewa saboda tsananin sanyin da ake batu wannan wuri na da shi, ƙila za a iya hura wuta a ji ɗimi. To ko kusa ba shi yiwuwa saboda binciken masana ya nunar da cewa, ba a samun makamashi a duniyar Mars, kuma babu nau'in iskar nan ta (Oxygen) a sararin samaniyarta. To ba ma wannan ba kaɗai, ko da mutum zai yi ƙoƙarin ɗaukar wani ɓangare na irin ƙanƙarar da ake samu a wanann duniya ya ce zai narka ta zuwa ruwa, ƙanƙarar za ta narke, to amma kuma mai makon ta zama ruwa sai ta zama iska duk dai sabo da rashin wasu sinadarai a sararin samaniyar duniyar Mars ɗin waɗanda za su ba da damar yin hakan.

Yanayin zafi ko sanyi na duniyar Mars

Duniyar Mars ta fi duniyarmu ta Earth sanyi matuƙa sakamakon nisan da duniyar ta Mars take da shi daga Rana. Matsakaicin yanayin da ake samu a Mars ya kai ƙasa da maki 60 a ma'aunin celcius (-60).

Mars na da iskar carbon dioxide mai matuƙar yawa wanda kaurinsa yana ƙasa da namu a nauyi, sai dai kaurin na iskar bai kai ya samar da yanayi kamar irinsu hadari da iska ba.

Yanayi na sararin samaniyar Mars yana sauyawa a lokacin da hunturu ke tursasa wa carbon dioxide ya bar sararin samaniyar Mars.

A baya, sararin samaniyar duniyar ta Mars na da nauyi matuƙa kuma yana har ruwa yana iya tafiya a kan duniyar. Bayan wani lokaci, abubuwa marasa nauyi a sararin samaniyar Mars sun gudu sakamakon ƙarfin iskan da ke tahowa daga rana wanda hakan ya yi tasiri ga sararin samaniyar duniyar ganin cewa Mars ba shi da ƙarfin maganaɗisu na riƙe abubuwa.

Sinadaran dake duniyar Mars


Rairayin kasar duniyar Mars kenan 

Duniyar Mars na da sinadaran Iron da nickel da sulfur. Mayafin da ya rufe Mars yayi kama da wanda ya rufe duniyar Earth wato (Ozone layer) wanda akwai dutse wanda ya ƙunshi silicon da oxygen da iron da magnesium.

Yadda ƙasar Mars take akwai duwatsu irin masu aman wuta waɗanda akwai irinsu a duniyar Earth da kuma duniyar wata.

Duniyar Earth kuma ta fi ƙunsar sinadarin earth da kashi 32.1 cikin 100 sai kuma oxygen da kashi 30.1 cikin 100 sai silicon kashi 15.1 da magnesium da kashi 13.9 da sulfur da kashi 2.9 da nickel mai kashi 1.8 sai calcium da kashi 1.5 da alminum da kashi 1.4 sai sauran kason 1.2 ya ƙunshi sauran sinadarai.

Wadannan sune bambance-bambancen dake tsakanin duniyoyin nan biyu. Allah ne masani.