Refrigerator (fridge)


Shin ko ka taba yin tunani ko mamakin game da yadda freezer wato firish ke aiki?

Freezer da Refrigerator zamu iya cewa na'u'rori ne na sanyaya ruwa ko dangin kayan abinci irinsu danyen nama, danyen kifi, kankana, lemo, mangwaro, kashu da sauran yayan itatuwa wadanda bazai yiwu a ajiyesu cikin yanayi mai zafi na tsawon lokaci ba.

Firish yana daya daga cikin manyan-manyan kayan amfani a cikin gida na yau da kullum, da wuya a wannan zamani ka sami gidan da babu freezer musamman a cikin alkaryu ba kauyuka ba, kodayake yanzu har wasu kauyuka ma akan sami wadanda ke amfani dashi.

Ajiye abinci acikin freezer ko fridge yana hana lalacewar abinci da kuma hana kwayar cutar bacteria hayayyafa.

Ta yaya freezer da fridge ke aiki?


Freezer yana aiki ne da taimakon abubuwa masu yawa wadanda aka ginashi dasu wato Components a turance, abubuwan sune kamar haka:

1. Compressor


Compressor tamkar shine zuciyar freezer. Yana taimakawa wajen juya akalar freezer gaba daya sai ya tattara karfi wato pressure cikin tukunyar dake samar da zafi a sashen kututturen lantarki wato circuit, batare da bata lokaci ba sai mizanin zafi ya samu cikin injin freezer. Kamar dai misalin yadda idan kana buga iska cikin tub na tayar keke da fanfon buga iska. Zaka rika jin fanfon yana kara daukar zafi yayinda ka takarkare kana bugawa na wasu yan mintuna, saboda an takure iska.

2. Condenser


Condenser yana makale ne a bayan refrigerator, Yana aiki ne wajen ingiza zafi na refrigerant zuwa wani sashe kamar na tururin iska ko burbushin ruwa, sanadiyyar zafin dake ficewa daga cikinsa sai tururin gas ya rika narkewa zuwa ruwa, wato ma'ana sai ya rikide daga tururin gas zuwa ruwa-ruwa.

3. Evaporator


Evaporator wani bangare ne wanda yake jone cikin refrigerator aikinsa shine sanyaya sassan frish ya dauki sanyi. Yayinda ruwa-ruwa na Condenser ya sauya zuwa tururin gas na evaporation sai nan take tururin ya sanyaya sashen da ake ajiye kayan abinci ko abin sha.


4. Capillary tube




Capillary tube wani dan siririn kwaroro ne ko tube wanda yake zama a matsayin gaba mai rarrabawa ko watsawa. Yana sarrafa burbushin ruwa-ruwa sai ya rika bi ta cikin kwaroron ya gangara zuwa sashe mai karancin pressure na cikin gabar evaporator.

5. Thermostat




Thermostat wani sashe ne mai sarrafa mizanin sanyi yana kuma bin diddigin yanayin temperature yana kashewa ko kunna compressor. Idan na'urar cikin Thermostat ta sunsino cewa mizanin sanyi yayi daidai a cikin freezer to sai ta kashe compressor idan kuma ta fahimci cewa yayi kadan sai ta kunna compressor ya ci gaba da aiki.

Fashin baki game da tsarin na'u'rorin sanyaya abinci

Muhimman sassan fridge


Hakika anyi aiki da basira wajen kirkirar freezer kasancewar yadda kowane sashe yana aiwatar da aikinsa cikin salo mai ban al'ajabi.

A takaice dai freezer yana aiki ne yayinda aka samu hadin guiwa na aikin na'u'rorin da aka dasa a cikinsa wadanda suke zama sanadin sauyawar burbushin gas zuwa burbushin ruwa ko kuma daga ruwa-ruwa zuwa burbushin gas wanda ake kira evaporation.

Kamar yadda muka karanta a sama a kalla wadannan na'u'rorin sanyaya abinci sun rabu gida biyu a turance wato freezer da refrigerator amma wani lokaci ana takaita sunan refrigerator da 'fridge' kawai duk yadda ka ambace su yayi duk da yake dai wadannan na'u'rori sunada banbanci a wasu bangarori musamman ta fannin siffa da karfin mizanin temperature da kowane guda yake samarwa.

Amma kuma ta fannin amfanin ko manufar kirkirarsu duka ya ta'allaka ne kacokan wajen sanyayawa da kuma bada kariya ta musamman ga abinci ko abin sha, ina tsammani wannan dalilin ne yasa Bahaushe baya tsawa wahalar da kansa wajen banbanta tsakaninsu shi dai kawai abinda ya sani Firish a jumlance.

Amma duk da haka zamu kawo banbance-banbancen dake tsakanin wadannan na'u'rorin masuburbudar sanyi.

Banbanci tsakanin Freezer da Refrigerator

To banbancin su dai duka bai wuce na masarrafar temperature ba wato Thermostat.

Freezer: An sana'anta shi yadda zai iya rike abinci sama da 18°C na ma'aunin Celsius yayinda za a yi ajiya mai tsawo wato na kwanaki masu yawa. Sa'annan temperature cikin freezer iri daya ne saboda haka duk abincin dake cikinsa zasu karbi sanyi a mizani iri daya ne Wato dai mu kaddara freezer tamkar gida ne mai daki daya babu wani lungu da sako a cikin dakin, dan haka duk abinda ke ciki abu guda zasu karba kai tsaye.

Wannan freezer kenan (duk kayan da aka zuba acikinsa suna daukar sanyi bai daya)


Refrigerator: An sana'anta fridge yadda zai iya ajiye abinci na mizanin ma'aunin Celsius tsakanin 0°C da 5°C wato 32°F zuwa 41°F kenan na ma'aunin Fahrenheit. Bayan haka kuma yana da sassa na abinci daban-daban, wato shi kuma fridge kamar gidane mai dakuna da lunguna kowane daki temperature dinsa da ban dana sauran dan haka kowane kalar abinci akwai adadin mizanin sanyi da zai iya karba dai dai da sanyin da aka samar a dakinsa.

Wannan fridge kenan (kowane sashe yana da adadin mizanin sanyi da yake karba)

Me yasa freezer keda matukar muhimmanci a rayuwar dan Adam ?

Ko shakka babu rayuwar dan Adam ta bunkasa tun lokacin da wannan fasaha ta kunno kai.

Kafin zuwan wannan fasaha mutane sun fuskanci kalubale mai yawa ta fannin ajiye abinci, akwai dabaru da dama da mutane suke yi don ganin sun adana abinci na tsawon lokaci amma abin yaci tura Misali, a da kafin zuwan freezer mutane suna shanya abinci ya bushe kamar irin su kifi da nama sai dai ba kowane jinsin abinci ne wannan dabarar zata karbeshi ba kamar misalin wasu dangin yayan itatuwa ba zai yiwu a busar dasu ba.

Haka nan daga cikin dabarun ajiye abinci a da mutane suna saka gishiri, ko su turara abinci da hayaki ko su killace da wasu muhimman murafa, ko busawar to amma fa duk da haka wadannan dabaru basu kai na fasahar zamani aiki ba.

Kadan daga cikin amfanin freezer sun hada da:

  • Ana safarar abinci zuwa waje mai nisa ba tare da ya lalace ba.
  • Farashin abinci ya sauka saboda wadatarsa.
  • Ana ajiyar iri na tsawon lokaci domin dasawa idan damina ta sauka
  • Rashin lalacewa ko rubewar abinci na tsawon lokaci
  • Freezer yana baiwa abinci babbar kariya na hana abinci kamuwa da guba
  • An sami fadadar hada-hadar kasuwancin abinci daga kasa zuwa kasa.