Fasahar IoT

Da farko menene fasahar IoT?

IoT wata sabuwar fasaha ce da aka kirkiro a yan shekarun nan na 1999 aka kuma assasata a 2010, fasaha ce mai matukar ban mamaki da burgewa gami da kayatarwa ta fannin inganta rayuwar dan adam a ban kasa.

Cikakkiyyar ma'anar IoT itace Internet of Things Fasaha ce wanda ta kai makura wajen nuna miyata da nuna kwarewa na masana fasahar zamani na wannan karni namu na kimiyya da fasaha.

IoT fasaha ce da aka kirkiro kuma aka sana'anta yadda kananan kayayyaki na gida zasu iya sarrafa kansu su rika karba da aika sako zuwa ga junansu ta hanyar internet batare da mutum ya sarrafa su ba.

A kasashen da suka ci gaba, kana iya samun gida mai dauke da hanyoyi da kayayyakin sarrafa gida masu amfani da tsarin Intanet. Misali, na’urar sarrafa talabijin a ko ina kake, ko sarrafa wutar lantarkin dake gidaje, daga wani wuri. Sai kaga mutum na zaune a ofishinsa, amma ya kunna wutar lantarkin dake dakinsa a gidansa. Ko ya kunna talabijin din gidansa ko kuma ya kashe, idan ya mance ya barshi a kunne, duk daga ofishinsa. Akwai kararrawa da ake jonawa a kofar daki ko kofar gida to yanzu akwai yadda ake iya hadata da wayar salalu ta yadda zaka iya sarrafata duk inda kake ta hanyar amfani da internet wannan ma duk misali ne na na'ura mai dauke da fasahar IoT.

Haka nan na'u'rorin IoT zasu iya sarrafawa gami da kula da dabbobin da aka ake kiwonsu a gidan gona da wata na'ura mai suna biochip transponder na'ura ce da ake sakawa cikin fatar dabba don tayi mata shaida wanda zata banbantata da sauran dabbobi yan uwanta, wato tamkar tana samar da identifications na kowacce dabba ba tare da an yanki kunnenta ko kahonta ko kuma daura mata wani zare don a ganeta ba,
to itama wannan naura tana daga cikin jerin na'u'rorin IoT.

KARANTA WANNAN: ► Menene Haske a mahangar kimiyya

Haka zalika akwai wata na’ura cikin motocin zamani mai sanar da direba idan iskar taya tayi kadan itama tana daga cikin internet of things.

Haka kuma motocin lantarki marasa direba (Driverless Cars) suna iya musayar bayanai tsakaninsu a ko ina suke, don gano bigire da tazarar ‘yar uwarta. Na’urori a asibitoci da manya da kananan makarantu na iya aiwatar da sadarwa tsakaninsu bisa tsarin fasahar IoT.

Yaya fasahar IoT ke aiki?


Na'u'rorin IoT wadanda ake aiki dasu a smart homes na zamani

Wannan fasaha ta IoT ta sami matsuguni ne karkashin fasahar 5G wato zango na 5 na karfin network na cellular. Su dai kayan masarufi na Internet of Things sun ta'allaka wajen iya sarrafa kansu ne yayinda suke jone a turken yanar gizo na IoT gateway. Wadannan na'u'rori suna dauke da wasu gaggan na'u'rorin yanar gizo irinsu sensor, processor da kuma gangar jikinsu (hardware) wanda an sana'antasu yadda kowane daya zai iya aiwatar da aikinsa ta hanyar aikawa da kuma karban bayanai ga junansu ta kafar internet.

Manyan wayoyin hannu na zamani wato smartphone suna taka muhimmiyyar rawa wajen inganta aikin IoT, saboda a ka'ida duk na'u'rorin IoT akwai application nasu acikin waya wanda mai su zai iya sarrafasu kai-tsaye ta cikin wayarsa.

Misali yayinda ka fita wajen aiki IoT device kamar freezer zata iya aika maka da sako ta cikin wayarka cewa mizanin sanyi ko zafi yayi yawa ko kadan, daga nan ofishinka zaka iya kashe na'urar batare dakayi tattaki ka koma gida ba.

Haka kuma akwai yar karamar na'ura ta IoT wanda likitoci suke dasawa a jikin maras lafiya na zuciya mai suna pacemaker

wannan na'ura tana taimakawa wajen daidaita bugun zuciyar dan adam, na'urar tana aiki da wireless network, wato tana iya aikawa da karbar sako daga clouds na yanar gizo. Shi yasa wadansu manazarta suke ganin yin amfani da wannan na'ura ajikin dan adam babbar barazana ce, saboda a kowane lokaci za a iya kutse cikin wannan na'ura.


Yadda ake dasa na'urar pacemaker a zuciyar dan adam

Bugu da kari manyan masana'antu suna girke na'u'rorin IoT don kara inganta kasuwanci na isar da kayan da kwastomomi suka saya garesu, wato na'urar dake iya sarrafa kanta wanda za a aiketa da kaya zuwa adireshin mai su ba tare da mutum ya sarrafata ba, duka wadannan suna daga cikin IoT devices.

Wannan kadan daga cikin irin fa'idojin wannan fasaha ta IoT kenan. Lallai wannan duniya da muke ciki ba aga komai ba tukuna in dai kayi tsawon rai a duniya to a kullum zakaga abubuwa ban al'ajabi na fasahar zamani. Allah yasa mu dace.

KARANTA WANNAN: ► Menene Guguwa a kimiyyance

Kada ku manta kuyi sharing ga abokanku a social media domin suma su amfana