Menene guguwa

To a takaice zamu iya cewa guguwa wata irin iska ce mai kadawa a murde da sauri da kuma karfin gaske takan yi rimi ta rika juyawa a bagire guda ko kuma ta rika gudu a murde irin misalin yadda agogo yake juyawa ko sabanin haka wato (clockwise or anticlockwise). Tana kadawa na wasu yan mintuna ko awanni. 


 Kwatankwacin yadda guguwa ke juyawa kenan

Wannan iska mai suna guguwa tana faruwa ne sakamakon sauyin yanayi na zafi ko sanyi da akan samu a sararin samaniya.

Karfin wannan iska yana iya bata damar daukar abubuwa manya ko kanana kamar irinsu ganyaye, burbushin kura, burbushin hazo idan tayi karfi sosai har tana iya dibar ruwa da kifaye ta tafi dasu. A wasu lokuta idan guguwa ta tashi a kusa da wuta takan debi harshen wuta sai ta rikide ta zama tamkar guguwar wuta.

Photo credit: National Geographic. Wannan wata guguwar harshen wuta kenan

Ire-iren guguwa


Guguwa ta rabu gida-gida akwai kananan guguwoyi akwai kuma  manya, sun dangata da yanayin musabbabin faruwarsu da kuma yanayin karfi ko saurin gudunsu. Ga bayanansu daki-daki kamar haka:

1. Karamar guguwa (Minor Windwhirl)


Wannan guguwa ce mai tashi akai-akai yayinda ake iska ko yayinda hadari ya taso ta kasance bata daukar manyan abubuwa sai dai kamar irin su shara, laidoji ganyaye da sauran kananan abubuwa, wannan shine yasa aka ayyanata a matsayin karamar guguwa wato minor whirlwind a turance. Irin wannan guguwar bata da wani hatsari.

Karamar guguwa 

2. Guguwar ruwa (Waterspouts)


Wannan guguwa ce mai tashi a cikin kogi ko teku, sam bata da alaka da sauyin yanayi daga gajimare na supercell kamar sauran guguwoyi. Waterspout takan debi ruwa tayi rimi dashi yayinda zata rika juyawa da ruwa da karfin gaske a cikin tsakiyar teku.

Waterspout tana faruwa ne yayinda iskar kusurwoyi biyu suka ci karo da juna a wata magama mai suna convergence line nan take zasu sarkafe juna sai su cure suyi sama saboda basu da wata hanya face sama a haka guguwar take ci gaba da wanzuwa tana dibar burbushin ruwa sai kaga tayi kaimi tana gudu cikin ruwa da masifar gudu an kiyasta wannan guguwa takanyi gudun kilomita 100 a cikin awa guda.

Guguwar cikin ruwan teku

Waterspout babbar barazana ce ga ma'abota tukin jiragen ruwa takan haifar da mummunan hatsarin jirgin ruwa, musamman kananan jirage irin su boat da canoe.

3. Mahaukaciyar guguwa (Tornado)

Wannan guguwa ce mai karfin tsiya da ban tsoro yayinda take mamaye sararin samaniya da wata irin siffa mai kama da curarren zoben hayaki mai fadin gaske, takan taso daga cikin gizagizai ta rika saukowa kasa har ta dire da dandamalin kasa, daga nan kuma sai ta zama kamar wani bangajejen bututu mai tsawo da fadi wanda ya tokare sama da kasa

Dubi yadda mahaukaciyar guguwa ke gangarowa daga gajimare na supercell har ta dire da doron kasa


Wannan guguwa sunan da aka bata ya dace da ita kasancewar takan yi awon gaba da duk abinda ta ci karo dashi komai girmansa, kamar misalin bishiyoyi da gine-gine ko gada ko motoci da sauran abubuwa masu tarin yawa.

Idan wannan guguwa ta gangaro daga sararin samaniya takan iya dibar ruwan teku yayin da mummunar ambaliya zata auku a teku sai kaga ruwa yana gudu cikin azababben gudu wanda ya wuce misali, ruwan yakan rusa birane da manyan itatuwa da manyan dogayen gine-gine. 

A sanadiyyar wannan guguwa akan tafka asarar rayuka da dukiya mai dinbin yawa. Irin wannan mahaukaciyar guguwa tana faruwa duk shekara a nahiyar Amurka musamman a yankin Oklahoma da New York da kuma yankin Tornado Alley.

Yadda mahaukaciyar guguwa ke aukuwa

Masana ilimin sauyin yanayi sun bayyana yadda tornado take faruwa wato musabbabin faruwarta kamar haka: 

Sun ce "idan  busasshiyar iskar dake cikin duniya ta haura sama cikin gizagizai sai ta ci karo da wata iska mai damshi wadda take ketowa daga cikin wani shamaki mai suna supercell dake cikin gajimare, wannan karon da sukayi shi zai haddasa murdewarsu sai su rika juyi suna gangarowa kasa har su dire a doron duniya to daga nan kuma sai mai aukuwa ta auku". 

4. Guguwar Sahara (Dust devil)


Guguwar Sahara (desert tornado) 

Wannan guguwa tana dibar burbushin kura da sauran tarkace marasa nauyi ta rika juyi tana gudu dasu wannan guguwa tafi yawan kasancewa a tsandauri ko sahara inda busasshiyar kasa take. Dust devil ba kasafai take zama mai hadari ba sai dai wasu lokuta takanyi karfi sosai har tayi barna.

 Tashin wannan guguwa a sahara babbar barazana ce ga fatake masu balaguro a kan rakuma musamman fatake a shekarun baya masu safarar kaya daga kasa zuwa kasa a rakuma, babban tashin hankali ne yayin da suka hangi wannan iska ta dumfari inda suke, saboda idan tayi karfi sosai tana iya rufe rukumi ko mutum da yashin data rarumo.

Kada ku manta kuyi sharing ga abokanku a social media domin suma su amfana