Hawainiya kenan (chameleon) a turance.

Hawainiya wata halitta ce daga cikin jinsin kadangarun iguana masu launin kala iri-iri. Wannan halitta tana daga cikin jinsin dabbobi masu dauke da nau'in jini mai sanyi wato cold blooded animals a turance.

Duk halittar dake da nau'in jini mai sanyi tana daga cikin jinsin kananan halittu na reptiles ko amphibians wadanda basa iya sarrafa akalar temperature na jikinsu da kuma muhallin da suka tsinci kansu dan haka basa bukatar zafi kuma ba zasu iya jure zama a kowane irin muhalli ba, sabanin sauran halittu wadanda ba reptiles ba wato mammals su sukan iya sarrafa zafi ko sanyin cikin jikinsu dai dai da muhallin da suka sami kansu a ciki, dan haka su zasu iya jure kowane irin yanayi.

Halittu jinsin reptile sun hada da kadangare, kulba, maciji, hawainiya, tsari, kada, kunkuru da sauransu.

To kaga idan ka duba itama hawainiya ta shigo cikin jerin reptile masu dauke da sassanyan kwayoyin jini.

Yaya hawainiya ke haihuwa

Wannan tambaya ce da mafi akasarin mutane suke bukatar samun amsar ta, saboda akwai shaci-fadi da ake yawaita yi musamman a kasar Hausa game da batun yadda hawainiya ke haihuwa misali akwai wadanda ke ganin idan hawainiya ta dauki ciki sai mijinta wai ya haka rami ya turata ciki da karfin tsiya ya binne ta a haka zata mutu a cikin ramin har ta rube daga nan kuma sai yayan dake cikinta su rika fitowa daya bayan daya sai su cigaba da rainon kansu har suyi girma.

To a gaskiya wannan ba daidai bane ba haka haiwaniya ke haihuwa ba. Masana ilimin kimiyyar dabbobi sun fayyace yadda tsarin rayuwar hawainiya take dalla-dalla.

To yaya abin yake?

Macen hawainiya tana haihuwa cikin hanyoyi biyu kodai ta hanyar saka kwai su kyankyashe ko haihuwa kai tsaye - Tsarin haihuwar yanada nasaba da irin jinsin hawainiya wato wasu kwai sukeyi wasu kuma haihuwa sukeyi kamar yadda sauran dabbobi ke haihuwa.

Jinsin hawainiya masu saka kwai ana kiransu Oviparous kuma sune jinsin da suka fi yawa sai jinsin masu haihuwa su kuma ana kiransu Ovoviviparous. Bayan saduwa da mijinta na wasu lokuta karanci sati uku (3 weeks) mafi yawa sati shida (6 weeks) - amma hakan yanada nasaba da jinsin hawainiyar, to daga bisani sai su saka kwai da yawa kimamin 20 zuwa 200.

Hawainiya jinsin panther idan cikinta yayi kwari sai ta daina cin abinci na tsawon kwana 10 zuwa 15, alamu ne dake nuna cewa lallai tana gab da saka kwayaye. Idan lokacin sakan kwan ya kusa sai ta nemi wani waje ta haka rami bayan ta gama sakawa sai ta binnesu zuwa wasu lokuta bayan sun kyakyashe sai su rika fitowa daga ramin.

Ga dabi'u da siffofinta kamar haka:

1. Takan saka kwai sa'annan kuma ta kyankyashe tsawon shekara biyu

2. Harshenta ya kasance dogo ya ninka gangar jikinta tsayi har sau biyu

3. Takan chanja kala da siffar irin duk muhallin data tsinci kanta sai ta saje zuwa kalar muhallin domin kubuta daga muggan kwari.

4. Tafi son kasancewa cikin ruwa mai gudana sama da wanda yake tsaye cik.

5. Suna da jinsi da ban da ban, akwai masu zama a kan bishiyoyi a dokar daji mai yawan ruwa (rainforest) akwai kuma masu zama a tudu ko kan tsaunuka.

Abincin Hawainiya

Dangin abincin hawainiya sune kwari da tsuntsaye. Takan yi sanda a hankalinki don farautar abincinta sa'annan sai ta zaro dogon harshenta ta cafko abin ta jawoshi zuwa bakinta ta hadiye kasancewar cikinta akwai sinadarin acid bada jimawa ba sai abinda ta hadiya ya narke.

Don samun cikakkiyyar koshin lafiya da kuma saurin girma hawainiya suna bukatar ruwa sukan yi amfani da dogon harshensu suna laso ruwa a haka suke sha iya daidai bukatarsu.

Inda Hawainiya ke rayuwa

Suna iya rayuwa dokar daji mai duhuwa da sarkakiya, ana kuma samunsu a sahara ko kan tsaunuka musamman a nahiyar Africa, Asia, Madagascar, Portugal da Spain. Suna zama a kan ganyaye da bishiyoyi wasu jinsin kuma a dandamalin kasa.

Dabi'un Hawainiya


Hawainiya tana amfani da dogon harshenta don cafko abinci daga nesa

1. Mafi akasari suna da doguwar wutsiya wanda suke nannadewa a reshen bishiya. Hannaye da kafafuwan hawainiya tafka-tafka ne masu fadi wanda ke taimaka musu wajen hawa saman itaciya ko dutse.

2. Bayan sauya kalar jikinta sa'annan kuma tana juya kwayar idonta domin ganin abinda ke bayanta saboda bata iya waiwayawa. Sukan hangi abu cikin sauri kamar misalin lens na cikin kyamara.

3. Suna daga cikin dangin dabbobi masu son kadaici. Macen hawainiya ba kasafai take bari namiji ya matso kusa da ita ba a mafi yawan lokuta sai dai yayin saduwa.
Namijin hawainiya mai cikakken kala shine yafi samun nasarar saduwa da macen hawainiya sama da kodadde mara kala sosai.

Tsarin Rayuwar Hawainiya

Gungun jariran hawainiya saman reshen bishiya suna shakatawa

Duk da yake hawainiya sun rabu jinsi-jinsi to amma duka sunada tsarin rayuwa iri daya. Duka sun ta'allaka ne kacokan a kan cin kwari kamar irinsu fari, farin danga, kudaje, filfilo, dokin almajirai (mantis) da kuma sauran kananan kwari. Idan har basu sami abinci ba to suna iya dogaro da ruwa kadai.

Rayuwar Hawainiya daga haihuwa zuwa mutuwa

Rayuwar hawainiya bata da banbanci da mafi akasarin sauran kadangaru. Yar jaririyar hawainiya takan yi saurin girma cikin wata 3 zuwa 12.

Haka nan kuma balagaggun yanyawa sukan cigaba da hayayyafa har zuwa lokacin mutuwarsu.

To akwai jinsin hawainiya da yawa wasu sukan dade wasu kuma basa dadewa a duniya.

Akwai sabubban da suke sawa hawainiya bata jimawa a duniya sune kamar muggan kwari masu cinyesu irin su macizai da tsuntsaye sun kasance babbar barazana ga rayuwar hawainiya. Sai kuma sauyin yanayi na muhalli da kuma wasu cututtuka da suke samunsu.

Hawainiya masu rayuwa cikin dokar daji sun fi fuskantar hatsari fiye da wadanda aka killace su a gida don kiwo, wadanda suke cikin daji duka-duka basa wuce shekara 2-3 a duniya.

Amma wadanda ake kiwatawa a gida suna dadewa sosai saboda sun kubuta daga sharrin muggan kwari da kuma sauran masifu.

Yanzu bari mu jero jinsin hawainiya da kuma adadin shekarun da sukeyi a killace.

►Jackson’s chameleon shekara 6 zuwa 10


►Veiled Chameleon shekara 6 zuwa 8+


►Panther chameleons shekara 3 zuwa 6+


►Carpet chameleons shekara 2 zuwa 3


►Fischer’s chameleon shekara 3 zuwa 5 


►Parson’s chameleon shekara 10 zuwa 20 


►Meller’s chameleon shekara 8 zuwa 12


►Senegal Chameleon shekara 3 zuwa 5 


A takaice wannan shine jerin tsawon rayuwar jinsin hawainiyoyi mabanbanta bisa la'akari da irin kulawar da suka samu.

Kada ku manta kuyi sharing ga abokanku a social media domin suma su amfana