Google Inc. Mountain View, California.

Kamfanin Google shine kamfani mafi girma kuma mafi shahara daga cikin tashoshin yanar gizo a duniya!

Mashahurin inji ne na bincike mai ban mamaki wanda miliyoyin masu amfani da intanet ke amfani da shi kowace rana wajen binciko abubuwan da suke bukata daga taskokin yanar gizo!

Shi dai Google wani injin bincike ne wanda duk wani mai amfani da intanet ke bukata don taimaka masa wajen binciko bayanan da yake nema daga shafukan intanet mabanbanta. 

Da zarar mai bincike ya rubuta abinda yake nema cikin akwatin bincike nan take injin Google zai tattaro bayanai wadanda ke da alaka da abinda kake nema cikin rabin sakan daga rumbunan shafukan intanet sai ya jibge maka su, babu abinda ya rage maka illa iyaka ka cigaba da bankadawa kana nazari a wadannan makalai (links) har ka zakulo shafin da ya dace da abinda kake nema.

Wanene ya kirkiri Google?

Sergey Brin da Larry Page sune suka kirkiro Google a shekarar 1998 lokacin suna daliban PhD. a jami'ar Standford dake California. Amma daga bisani an sami wasu canje-canje game da mallakar Google.


Sergey Brin da Larry Page Kenan

A farkon fari kamfanin Google ya kasance kamfani ne na cikin gida wato na kasar California ita kadai, an kaddamar da kasancewarsa kamfanin riko na California ranar 4/9/1998 wanda daga bisani aka kaddamar dashi a matsayin na bainar jama'a a watan August,19,2004 tun daga wannan ranar aka maida hedkwatarsa zuwa birnin Mountain view dake kokuwar birnin California, mai lakabi da googleplex

KARANTA WANNAN: ► Cikakken Bayani Game Da Na'ura Mai Kwakwalwa

A takaice dai sannu a hankali kamfanin Google ya ci gaba da samun daukaka a duniya. kamfanin ya mamaye gurbi mai girma a intanet. 

Abubuwan da Google ya mallaka sun hada da: Manhajar wayar Android, Google search, Youtube, Gmail, Play store, Google chrome, Google drive, Google slides, Google calendar, Google docs, Google sheets, Duo, Hangout, Google plus, Google Earth, Google postcard, Blogger, Google translate da kuma dinbin wasu ababen.

Wanene shugaban Google a yanzu?


Sundar Pichai Kenan shugaban Google

Mr. Sundar Pichai shine shugaban Google a yanzu ya zamo shugaban kamfanin ne bayan da a ka kirkiro uwar kamfanin mai suna Alphabet. Shi dai Pichai dan asalin kasar India ne shine yake rike da madafun iko na kamfanin Alphabet kafin daga bisani aka zabe shi ya zama shugaban Google a yau.

Karfin tattalin arzikin Google


Google economic impact

Wadanda suka kirkiro kamfanin na Google Larry Page da Sergey Brin sun tara arzikin da ya kai dala biliyan 34.6 da kuma dala biliyan 33.9, kamar yadda mujallar da ke bayyana attajiran duniya ta Forbes ta wallafa.

Pichai ya zama zakaran gwajin dafin attajiran duniya a yau, yana daga cikin miloniyoyi na duniya kasancewar yawan hannun jari da ake bashi, Wannan kyautar hannun jarin da ake bawa Mr Pichai ta sanya hannun jarinsa ya karu inda ya kai dala miliyan 650.

An cigaba da rinka bawa mr Pichai ikon mallakar hannun jari a dukkan wattani uku na shekara har zuwa karshen shekarar 2019.

Kada ku manta kuyi sharing ga abokanku a social media domin suma su amfana