Kiwon kifi alheri ne

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah mahaliccin komai. Tsira da aminci su tabbata ga Annabin rahma da iyalansa da bayi nagari wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar alkiyama.

Menene Kiwon kifi?

To da farko dai idan mu kace kiwon kifi to wannan na nufin hanyar sarrafa kananan kifaye ta hanyar basu kulawa har sukai munzalin balaga, ta yadda zasu cigaba da hayayyafa su kara yawa, wanda dama wannan shine babban dalilin kiwon nasu.

Shin ko akwai kalubale a kiwon kifi

Kamar yadda muka sani bisa al'ada kusan kowace irin sana'a tana cike da kalubale da matsaloli masu dinbin yawa dole sai anyi hakuri gami da juriya musamman a lamari wanda ya shafi kiwo.

Atakaice dai zamu iya cewa hakuri shine makami kuma jigon nasarar manomi, kaga a misali Bafulatani mai kiwon shanu a kullum sai ya fitar da shanunsa zuwa kiwo, komai sanyi, komai ruwa, kuma komai zafin rana bazai huta ba koda na rana guda dole sai ya fita kiwo, a haka zai cigaba da rainonsu yana basu kulawa shekara da shekaru har sukai daruruwa Zuwa dubunnai ba don komai ba sai don ya jure ya kuma yi hakuri da irin kalubalen daya fuskanta.

Haka zalika mai kiwon kaji shima dole kullum sai ya tsaftace makwancinsu sa'annan ya zuba musu sabon abinci da safe, da rana da yamma batare da gajiyawa ba.

To haka mai kiwon kifi wajibi ne sai ya zama mai juriya kafin ya kai ga nasara. Hakuri da bin komai sannu a hankali shine babban makami a sana'ar noman kifi

YADDA AKE FARA NOMAN KIFI


To noman kifi dai iri-iri ne akwai hanyoyi daban daban na noman kifi saboda dalilan kiwonsa na kara yawa a kullum a duniya.

Kadan daga cikin dalilan kuwa sune kamar haka a kullum ana samun karuwar adadin jama’a mabukata kifi da sauran albarkatun cikin ruwa wadda suke amfani dashi a matsayin abinci ko kuma sana'a wadda zasu dogara da ita, bayan haka mutane na kara fahimtar muhimmancin cin abinci mai dauke da kifi a ciki.

Maganin zaman kashe wando, kamar yadda muka sani rashin aikin yi da zaman kashe wando yayi kamari a cikin matasa musamman dalibai wadanda suka kammala karatunsu amma basu sami aikin yi ba, to daga ire-iren wadannan matasa akwai masu zuciyar neman na kansu dan haka suke ta'allaka a noman kifi domin samun rufin asiri.

Mutane da dama dai kowa yana noman kifi ne a bisa ra’ayinsa kodai dan a ci ko a sayarwa dan samun biyan bukatar rayuwa ta yau da kullum, ko kuma saboda nishadi, wasu kuma suna noman kifi ne don ilmantarwa musamman a manyan makarantu don koyar da dalibai yadda ake kiwon a aikace wato (Practically).

Matakan farko na noman kifi sune kamar haka


1. Ka tabbatar ka tantance irin gonarka, wato inda zaka noma kifin shin a bayan gida ne? ko kuma a tafki ne? sa'annan yaya wajen yake ta fuskar yanayin zafi ko sanyin wajen.

Sa'annan dole sai ka zayyana dalilin da zai sa ka fara noman kifin wanda ta hakane zaka fi samun cikakken kwarin guiwa a harkar.

Bayan haka dole ka tantance irin kalar kifin da kake so ka kiwata saboda akwai hanyoyi iri iri wajen noman kifi, saboda haka akwai bukatar sanin wanne irin kifi kake so ka noma, da kuma rubuta tsari da manufofinka na kiwon.


Duk mai bukatar ya fara wannan sana’a yana bukatar amsa wadannan tambayoyin:

a. Me zaka yi da kifin bayan ka noma? Abinci za’a yi da shi, sayarwa, ilmantarwa ko kuma kawai don kawa (kwalliya)?

b. Shin kana da nufin gina dan karamin tabkin kifi da kanka ne, ko kuma niyyar ka itace kafa katafaren kamfani domin samun riba mai yawa da shahara a duk fadin duniya?

2. Ka tantance irin jinsin kifin da kake so ka noma. Saboda tabkin noman kifin da zaka gina ya danganta ne da irin kalar kifin da zaka noma.

Sa'annan kuma akwai bukatar fahimtar wadannan:

a. Idan har ka fara tantance irin kifin da kake so ka noma, to akwai bukatar tuntubar wanda yake noma irin wannan kifi domin su baka karin haske akan yiwuwar sa da irin karfin da kake da shi. Domin masu iya magana sun ce da nagaba ake gane zurfin ruwa.

b. Ka rubuta kuma ka tantance duk kudin da ake kashewa akan kowanne irin jinsin kifi, kuma ya zama wajibi kasan cewa farashin kowane daga ciki ya sha banban da kowane irin jinsin kifi da zaka noma.

c. Ka kuma yi la’akari da irin yanayin da kake so ka noma kifi. Akwai kifin dake bukatar ruwa mai sanyi, akwai kuma mai bukatar ruwan dumi saboda haka kana bukatar gujewa duk wani kasha-kashen kudi dake da alaka da salon sanyayawa ko dafa ruwa.

KADA KA KARAYA AKAN NEMAN ILIMIN KIWON KIFI

Idan kai bako ne a wannan fanni, to kana bukatar samun fahimta da kwarewa a wannan fanni na neman karin haske daga manoma wadanda sun dade a harkar kafin ka fara naka.

kodayake alal hakika kiwon kifi ba ya bukatar wani kudi mai yawa kafin fara shi. Sai dai ya danganta da karfin aljihunka da kuma kwatankwacin yadda ka ke son ka aiwatar da shi. Kamar yadda masana a fannin ke bada shawarar farawa da karamin jari shi ya fi.

Ba komai ya sa masanan bada wannan shawara ba, sai dai farawa daga mataki na kasa zai baka damar fahimta tare da kwarewa kafin ka tsunduma ga mataki na gaba.

Ko da ka taba harkar, mallaka da kuma tafiyar da gonar kifi na bukatar ilimi mai yawa akan yadda sana’ar take.

Idan kuma niyyar ka itace ka mallaki sana’ar, sannan ka ringa lura da bangaren sha'anin wannan gona, to hakan ma yana bukatar ka fadada iliminka akan sana’ar sannan ka dauki mutum wanda yafi kuzari a cikin ma’aikatan ka domin tafiyar da wannan harka sai an sami mutum tsayayye mai juriya.

Tafkin kiwon kifi don ado

Ga wasu hanyoyin neman ilimin noman kifi a takaice:

a. Ka nemi aiki a gonar dake noma irin jinsin kifin da kake da niyyar nomawa. Hakan zai taimaka ka kara fadada iliminka ta fannin sanin dabi'ar kifayen, da kuma sanin tsarin rayuwar kifayen.

b. Ka nemi ilimi akan yanar gizo da littatafan da aka buga wadanda mafi yawancin su na binciken bayanai takai-mai-mai akan yadda ake noman ire-iren kifaye.

c. Ka lazimci kasancewa ajujuwa a jami’a ko makarantu musamman akan noman kifi. Wannan yana da matukar amfani idan aka yi da wuri, saboda zai fede maka biri har wutsiya akan wannan sana’a baki dayan ta.

ABUBUWAN DA AKE BUKATA DON KIWON KIFI

Yanki mai yawan ruwa marasa kafewa

Kafin a fara noman kifi, dole manomi ya tabbatar ya tanadi wadannan abubuwan:

1. Tsabtataccen ruwa mara yankewa, ko dai ta hanyar amfani da bututun zuba ruwa ko kuma ta hanyar rijiyar burtsatse.

2. Samar da lafiyayyar hanya wacce zata saukake shiga da fice daga gonar.

3. Bayan haka kuma ya kamata a ajiye gonar kusa da kasuwa domin saukake shige da fice da iya hanzarta kai kifi kasuwa (idan bukatar hakan ta taso) don kiyaye lalacewarsu.

4. A tabbatar an yi gonar a wurin da yake fili ne kuma a kiyayi yin gonar a kan tuddai.

5. A tabbatar da sa ido a gonar wato ta sami cikakken kulawa.

6. Irin kifi da za a zuba ya kasance irin da ke da juriyar karancin iska ne kuma irin wanda ke matukar bukata.

ZABEN FILIN KIWON KIFI MAFI DACEWA


1. A nemi fili marasa tudu, kuma a guji wuri mai yawan tuddai dame daji-daji domin gyaransa zai haifar da karuwar kudin noman. A saukake zaka iya gina kududdufin kiwon a bayan gidanka don samun saukin kulawa.

2. A nemi wurin da ke da saukin shiga da abin hawa don shiga ko fita da kifin domin hana saurin lalacewa.

3. Dole kuma ya zama babu matsalar ruwa a wurin don hana yawan asara.

YADDA AKE GINA TAFKIN KIFI

Yi nazari akan hotunan dake kasa, tun daga matakin farko har zuwa na karshe. Hakika gina tafkin kifi yana bukatar kwarewa da kuma kayan aiki managarta.

Ka tabbatar ka cire sauywoyi da sauran ciyawun dake wajen kaf



2. Bayan ka gama share filin kuma ka gama gwaje-gwaje, to sai ka fara gina rami kana fitar da kasar gefe ta yadda zaka fitar da siffar ramin


3. Mataki na gaba shine gwada fasalin tsayi da fadin tafkin
4. Ka gwada tsayi da fadin kowacce kusurwa cikin hikima


6. Ka tabbatar ka daidaita tudun ramin kada ya gaza 1.5 metre
7. Bayan ka kammala ginin tsayi da fadin ramin sai ka zana magudana daga tsakiyar ramin wanda zaka rika fitar da lalataccen ruwa da sauran datti.


8. Sassan kammalallen kududdufin kiwon kifi na zamani.

Back button               Next button


KARANTA WANNAN: ► Koyi Yadda Ake kiwon Kaji A Zamanance



Kada ku manta kuyi sharing ga abokanku a social media domin suma su amfana