Bitcoin kenan

SHIN KASAN MENE NE BITCOIN???


Bitcoin wani tsarin kudi ne da ake amfani da shi a intanet kadai, kuma yana amfani a duk duniya ta hanya bai daya, kuma babu wani banki guda daya da yake kula da wannan nau’in kudin.

 Wani masanin fasaha mai suna Satoshi Nakamoto ne ya kirkiro fasahar Bitcoin a shekarar 2009, kuma masu ta’ammuli da nau’in kudin suna yi a tsakanin su ba tare da wani mutum na uku ba wanda zai lura da ta’ammulin tsarin. Sakar sama na intanet ne kawai ke kulla ta’ammulin.

Ana yin amfani da kudin Bitcoin wajen musanyar kudade a kafar intanet, ana iya siyan hajoji ma, a shekarar 2015 kadai ‘yan kasuwa kimanin 100,000 ne suka yi mu’amala da kudin Bitcoin, ana iya amfani da kudin na Bitcoin domin zuba hannun jari a wasu kamfanoni.

A wani bincike da jami’ar Cambridge ta gudanar a shekarar 2017 ta gano akwai akalla kusan mutum sama da miliyan biyar da suke amfani da kudin na Bitcoin.

Ta Ya Ya Wannan Nau'in Kudin Yake Aiki?



Wannan itace tambayar da kowa yake yi in ya ji maganar wannan nau’in kudin, kamar dai yadda wadanda su ka san yadda ake kulla cinikayya ta kafar intanet, mutum zai sayi abinda yake so sai ya biya ta account dinsa a shagunan da suke kafar intanet (Online Stores).

To haka shima Bitcoin ake cinikayya da shi akwai shagunan kafar intanet da suke yarda da cinikayya da nau’in kudin na Bitcoin, ta yadda mutum in ya ga abinda yake sha’awar siya a shagunan kafar intanet da suke karbar nau’in kudin sai kawai ya shiga bayanen jakar ajiyar kudin shi na Bitcoin (Wallets) a take zasu cire kudin su daidai da cinikayyar da ya yi.

A takaice....

Bitcoin wani nau'i ne na kuÉ—in intanet. Ba shi da siffa ta zahiri. Madadin haka, ana sayar da rukunin kuÉ—in a intanet da sauran shafukan sada zumunta

Ba shi da wata iyaka, ma'ana iya shafukan da za a iya amfani da su, sannan ba su da banki, kamar kudin zahiri da aka sani.

A maimakon haka, yana aiki ne a hanyoyin intanet da wasu dubban na'urori da ke hadawa da ajiye bayanan yadda ake kasha kuÉ—in.

Dubban na'urorin ke hana samun bayani dangane da yadda kuÉ—in ke shiga da fita - amma akwai wata fasaha da ake kira 'blockchain' da ke iya ba da damar gano shiga da fice kuÉ—in.

Blockchain bayanai ne da ake iya aikawa kan yadda aka kashe bitcoin - yana hana wani 'kashe kuÉ—in bitcoin sau biyu' kuma zai yi matukar wahala wani ya iya sauya bayanan shige da ficen kuÉ—in. Da wahala, a iya cewa ma ba zai yiwu a sauya shi ko a wawushe shi ba.

Daga ina ya samo asali?



An fara wallafa Bitcoin ne a wani jerin sakonni na intanet ga masana kimiyyar komfuta da ke karantar yadda za a iya aika sako ta intanet cikin tsaro a 2008.

Wanda ya fara wallafa shi na da wani suna na bogi Satoshi Nakamoto amma babu wani mutum ko mutane kawo yanzu da aka tabbatar shi ne Satoshi.

Ana amfani da shi har yanzu kuma a ina ake amfani da shi?

Ana amfani da Bitcoin har yanzu kuma ana sayen shi a matsayin kuÉ—in da ba na zahiri ba, wanda ke ba masu amfani da shi damar sauya kuÉ—in zahiri da aka saba da shi zuwa bitcoins.

Don amfani da Bitcoins, matakin farko shi ne bude abin da ake kira 'wallet' ko lalita (wadda ke iya zama a intanet ko a manhajar waya ko a wata na'ura mai tsaro). Wannan na kare duk wani sirri da ake amfani da shi wajen hadahadar bitcoins.

Lalitarka za ta kunshi 'adireshi' wanda yake aiki kamar lambar asusun banki sannan ana iya amfani da shi wajen karbar bitcoins. Haka kuma zai kunshi password din da ake bukata wajen aika bitcoins (ana kiran wannan private key).

Idan ka manta da wannan private key din, ko kuma aka sace, kana iya rasa bitcoins dinka, kamar dai yadda idan ka batar da lambar ka ta PIN ta katin ATM.

Me zai sa mutum ya fi son Bitcoin maimakon kuÉ—in da aka sani?

KuÉ—in da muke amfani da shi a yau na da tarihi da daban idan aka yi batun kuÉ—i, wato ba abu ne mai wahalar samu ba kamar sulallan zinare.

Yanzu idan ka duba abin da aka rubuta a kan £10: "Na yi alÆ™awarin biyanmai wannan kudin fam goma da zarar ya tambaya."

Wannan ba wani alkawarin a zo a gani ba ne idan ka duba cewa abin kawai da hukumar da ke kula da kuɗin (kamar Babban Bankin Ingila) za ta yi shi ne ta sake buga wani kuɗin don cika wannan alƙawarin.

Yayin da ake sake ƙirƙirar kuɗi, yana rage daraja kuɗin da ake da shi. Ba lallai ne mutane su gane wannan raguwa a darajar kuɗin ba saboda kuɗin na nan yadda suka san shi; amma za su iya lura cefanen da suke yi duk mako da farashin abincin da suke saye na ƙaruwa.

A nan ne Bitcoin ya sha bamban.

Ana samar da bitcoin ne sannu a hankali kuma a ƙayyade, sannan babu wanda zai iya ƙirkirar bitcoin a lokacin da ya so.

Ba a taɓa iya samar da bitcoin sama da miliyan 21 ba; kuma ana iya raba ko wane bitcoin zuwa kashi miliyan 100, wanda ake kira Satoshis. Wannan zai hana raguwar darajarsa kamar yadda kudin da muka sani ke yi (lamarin da 'yan Zimbabwe da Venezuela suka fi kowa sani).

Bitcoin na iya mayar da kai miloniya?

Bitcoin kadara ce mai hatsari. Kamar ko wane hannun jari, yana faÉ—uwa da tashi kuma ya danganta da lokacin da ka siye shi. Yana iya mayar da kai miloniya kuma yana iya talauta ka.

A farko farko, an sayar da Bitcoin daya kan $1; farashinsa ya hau kusan $20,000 ko £15,400 a 2017 kafin farashinsa ya faÉ—i warwas zuwa kusan $3,000 ko £2,300 sannan ya koma $8,000 ko £6,200.

Me ake nufi da haƙar bitcoin? (wato bitcoin mining)

Bitcoin mining

Kalli bidiyon dake kasa, zai taimaka maka sosai wajen fahimtar abinda ake nufi da Bitcoin mining

Haƙar bitcoin na nufin samar da sabbin bitcoin ta hanyar amfani da wasu abubuwa da ake kira 'blocks'.

Ko yaushe a faɗin duniya akwai gasa da ake yi wadda ake kira 'gasar haƙa' don lashe damar ƙara 'block' ga 'blockchain' wato jerin ko tarin 'blocks'.

Shiga gasar na buƙatar masu amfani su sayi wata na'ura da aikinta shi ne kawai 'hakar' bitcoin wadda kuma take shan wutar lantarki sosai.

Ana iya cewa ma an fara daina yayin na'urar saboda sabbin ƙirƙire ƙirƙire da ake ci gaba da yi don haka hakar bitcoin bai fiye kawo wa mutane riba sosai ba.

Mutanen da ke wannan aikin ana kiransu masu haƙar bitcoin. Suna shiga wannan gasar ne saboda abu biyu:

Don su samu riba (a halin yanzu ribar bitcoin 12.5) da ake bai wa duk wani mai haƙar bitcoin.

Haka kuma, haƙar na ƙara wahala idan mutane da yawa suka sa hannu; ana haka ne don a takaita bayar da sabbin bitcoins cikin gaggawa.

Haka kuma, ribar ko wane 'block' na raguwa da rabu duk shekara 4, wannan na sa wa samar da su ya ƙara tsada.

Shin muna iya amincewa da kuÉ—in bitcoin?

Kamar ko wace sabuwar ƙirƙira da ke ci gaba, akwai mai inganci akwai masu ƙarancin inganci.

A fagen kasuwanci irin wannan na fasaha, mutane da yawa na shan wahalar fahimtar wane bitcoin ne mai inganci sannan ba kowa ne ya gama fahimtar yadda su ke aiki ba da sahihancinsu.

Wani lokaci, tsare tsare kamar One Coin sun yi iƙirarin kasancewa kuɗaden bitcoin amma daga baya aka gano na bogi ne.

KuÉ—in bitcoin na iya shahara fiye da kuÉ—i na zahiri nan gaba?


Na'u'rorin hakar bitcoin

Ana iya hasahsen haka, amma akwai yiwuwar za a iya kwashe kwanaki tsawon shekaru kuma sai an duba abubuwa sosai da suka shafi tattalin arziƙi da shari'a kafin a cimma haka.

Misali, 'blockchain' na Bitcoin a yanzu ba sa iya daukar shige da ficen bitcoin da yawa idan aka haÉ—a da yadda ake amfani da kuÉ—i ta hanyar intanet kamar Visa da Mastercard.

Wani É“angare na kuÉ—in intanet da ke shahara kuma ke da yiwuwar shahara fiye da kuÉ—i na zahiri shi ne 'stable-coins', wanda ake alakanta darajarsa da kuÉ—in da muka saba amfani da shi kamar dalar Amurka da Euro da Fam, ba kamar bitcoin ba, yadda ba a iya cewa darajarsa É—aya ta kai £26,000 a wannan shekarar sannan bayan shekara biyu a cewa ya faÉ—i ya koma £6,000.

Yaya ake sayen bitcoin?

Ana sayen waÉ—annan kuÉ—aÉ—e na lantarki don a sayar da su ga wasu duk lokacin da buÆ™atar hakan ta tashi. Saboda yadda waÉ—annan kuÉ—aÉ—e suke tashi, misali yadda Dala (Dollar, $) take tashi a yanzu, sayenta zai iya zama riba ga mutum – ta yadda za a saya kashegari kuma a sayar musamman idan ta Æ™ara kuÉ—i. Haka nan ita ma wannan harkar take.

Ta Yaya Za a Fara?

KuÉ—aÉ—en lantarki na wannan harkar ta cryptobusiness suna da dama, a cikin mafiya shahara sun hada da:

KuÉ—aÉ—eAdadin KuÉ—in LantarkiFarashin KuÉ—i a Naira
BitcoinBTC 0.00005383₦1,000
LitecoinLTC 0.012274₦1,000
EthereumETH 0.001682₦1,000
Bitcoin CashBCH 0.00459₦1,000
RippleXRP 6.10₦1,000


…da sauransu.

Abun ake fara yi da farko shi ne, a matsayin mutum na ɗan-koyo sai ya dubi wanne ya kamata ya fara saya a cikinsu? Sannan kowane akwai tsarukan yadda ake amfani da shi da yadda ake kasuwancinsa. Idan aka ɗauki Bitcoin musamman yadda yake ruruwa kullum a kasuwa, zai fi sauƙin harkar sai dai yana da tsada. A yanzu haka Bitcoin 1 ya kai N18,670,562. Ana lissafinsa da 0.1 zuwa sama. Sannan ana buɗe masa asusu da ake ƙira wallet a shafukan da ake harkar. Haka nan su ma sauran kuɗaɗen lantarkin kamar su Ethereum, Litecoin da sauransu.

Yaya Ake Fara ‘Bitcoin Trading’/‘Cryptobusiness’

Wasu lokutan mutane suna ruɗuwa daga jin sunan Bitcoin Mining, Bitcoin, CMDX, Bitcoin Trading, Cryptocurrency da sauransu. Bari in kore shakkun: duk harkar ɗaya ce, dukkaninsu kasuwancin lantarki ne da ake ƙira Cryptocurrency ko Cryptobusiness sai dai bambancin tsari kawai.

Bitcoin sunan kuÉ—in lantarki ne. Bitcoin Trading kuma shi ne kasuwancin Bitcoin, yadda ake juya Bitcoin É—in ya koma riba. Misali idan aka sayi na ₦1,000 yadda za a mayar da shi na N1,500.

To a kullum ina bada shawarar cewa duk abunda za a yi to a yi bincike a kanshi kada a fada kai-tsaye. A nan nake cewa abu na farko da ya kamata a yi tunda an fahimci mene ne Bitcoin kuma mene kasuwancin lantarki wato cryptocurrency, to a ƙara faɗaɗa bincike ta yadda za a ƙara sanin wasu muhimman abubuwa game da lamarin a wurin wasu.

Abu na biyu kuma shi ne buÉ—e asusu wato wallet, wanda za a rinÆ™a amfani da shi wajen karÉ“ar kuÉ—i da tura shi. A Nigeria idan za a yi harkar nan zan bada shawarar ayi amfani da asusun Luno, wanda mutum zai iya sayen kuÉ—in lantarki kuma ya sayar ko yana kwance a É—akinsa. Yadda tsarinsu yake shi ne, mutum zai iya neman sayen Bitcoin (ko wani nau’in kuÉ—in lantarki daban) ta hanyar sayensu da kuÉ—aÉ—ensa na banki kuma ya biya da katin cirar kuÉ—insa. Akwai hanyoyin biyan kuÉ—i da suka haÉ—a da biya da Paystack; wanda ya kasance dama ne da ke shiga tsakanin kamfanin da za biya kuÉ—i da bankin mutum.

GARGAƊI: babu yadda za a iya yi wa mutum sata a asusunsa ba tare da ya ba da haɗin kai ba. Kada wani ya ɗauki lambobin asusunsa ya bayar ga wani face sahihan kamfanoni. A tabbatar wani bai ƙira mutum yace ya faɗa masa lambobin sirrinsa, kuma ya ɗauka ya bayar ba.

Idan ba a gida Nigeria ba ne, ko kuma wani dalili daban akan iya amfani da asusan Coinbase ko na Binance.

Yadda Za a yi Rajista da Asusun Luno.

Kamar yadda na ce asusun Luno yana da sauƙi musamman idan mutum yana son kasuwancin gida Nigeria, sannan yana da wasu alfanu da yake ba wa mutumin da ke amfani da shi. Abunda za a yi shi ne rajista da wannan asusun ta hanyar ziyartar shafinsu na yanar gizo https://www.luno.com wanda daga nan za a shigar da adireshin imel da lambobin sirri, sannan sai su tura saƙo zuwa adirenshin imel ɗin don tabbatarwa.

Bayan an yi rajista da Luno kuma an tabbatar da shaida, abu na gaba shi ne jarraba sayen kuÉ—in lantarki domin komai sai an jarraba shi a kan dace. Za a iya sayen kuÉ—aÉ—en Bitcoin, Litecoin, Ethereum, Bitcoin Cash da Ripple a wajensu kuma a biya kai tsaye cikin sauki.



Sannan kamar yadda wannan hoto na ƙasa ya nuna yadda na buɗe akawunt da asusun Luno, kuma na buɗe asusun Bitcoin (za a iya gani a BTC 0. 000000 a ƙarƙashin kalmar Cryptocurrency)


Wato duk kuɗin lantarki da za a yi musayarsa (kasuwancinsa) sai ya kasance yana da asusu wato an buɗe masa wallet kamar su Litecoin ko Ripple kamar yadda yake a hoto na sama Add a new wallet (a ƙarƙashin kalmar Cryptocurrency) A hoto na ƙasa kuma an nuna waɗanne kuɗaɗen lantarki ne za a iya buɗe musu asusu wato wallet da Luno:



Bayan an buÉ—e asusu za a iya shigar sa a inda za a ga babu komai a cikinsa, kamar yadda wannan asusun Bitcoin É—in yake:



Sannan idan aka danna BUY BTC a hoton da ke sama za a shigo nan inda za a iya saya ta hanyar biyan kuÉ—i kai-tsaye:




Kamar yadda ake gani a sama, za a iya saya da kuɗaɗen Nigeria (kuɗaɗen mutum na banki) ta hanyar danna NGN Wallet. Sannan a ƙara dannan Top up Wallet kamar yadda ake gani a hoto na ƙasa:



Sannan a nan kuma za a ga yadda za a iya biya ta hanyar amfani da Paystack da katin cirar kuÉ—in mutum na ATM:



Idan aka shiga sai a shigar da adadin kuÉ—aÉ—en da ake so a saya, misali ₦2,000 ko sama da haka. Za a iya sayen na N10 zuwa ₦100,000 a lokaci guda.

Abu na gaba shi ne amfani da code din mutum domin tara kuɗaɗe. Kamar yadda yake a hoton da ke ƙasa, za a iya ganin yadda idan an shiga Rewards inda aka ajiye waɗannan lambobi QKNFPZ, kuma a ɗaya gefen akwai Enter a Code, wanda nan ne inda za a sanya code ɗin:



Idan aka sanya waÉ—annan code É—in, shi mai asusun (wato wani abokinka da ya gayyace ka) zai samu ₦250 a asusunsa kuma kai ma ka samu.



Don haka idan ka ji daÉ—in wannan rubutun ka sanya wannan code É—in nawa a wannan sashe na ENTER A CODE.

Rubutu na gaba zamu yi bayani kan yadda za a iya sayar da kuÉ—aÉ—en lantarki ga wasu kuma a samu riba sannan a iya amfani da kuÉ—aÉ—en.

kai dai Cigaba da bibiyarmu a wannan shafin. Idan kuma akwai abinda baka gane ba zaka iya tambaya ta sashen comment a kasa ko kuma a tuntubemu kai tsaye ta shafin Customer's Support namu.

    Reference


>>>BBC Hausa


>>>Flowdiary


KARANTA WANNAN: ► Yadda Tsawa da Walkiya ke faruwa A Kimiyyance


Kada ku manta kuyi sharing ga abokanku a social media domin suma su amfana