Menene tauraron dan Adam?


Kumbo a sararin samaniya

Da farko dai, tauraron dan Adam shi ne duk wata na'ura mai cin gashin kanta da ake harbawa zuwa sararin samaniya don mikawa da karbo bayanan yanayi ko dauko hotunan wasu wurare da dan Adam ba ya iya kaiwa gare su ta dadi ko kuma sunsuno irin yanayin da muhalli zai kasance a wasu lokuta na daban ko kuma don yada bayanan sadarwa daga wani bagire na duniya zuwa wani bagiren.

Ire-iren wadannan taurari suna shawagi ne a cikin falakin wannan duniya tamu ko duniyar wata da taurarin da Allah Ya halitta, ko kuma cikin falakin wasu duniyoyi makamantan namu.

A halin wannan shawagi ne suke gudanar da ayyukansu na nemo bayanai, ko karbowa daga wani bangaren wannan duniya don yada bayanan zuwa wasu bangarorin daban, ko kuma nemo bayanan da ke da nasaba da falakin da suke shawagi a ciki, don aiko sakon da suka taskance zuwa gare mu a wannan duniya, ko kuma a wasu lokutan, su dauko mana hotunan abin da ke faruwa ga manya-manyan tekunan da ke zagaye da mu a duniya gaba daya.

Yaushe aka fara harba tauraron dan Adam sararin samaniya

An fara harba ire-iren wadannan taurarin wucin-gadi ne zuwa cikin falaki shekaru kusan hamsin da tara da suka gabata (1957), kuma ya zuwa yanzu, an harba wajen dubunnai masu zuwa don karbowa da aikawa da bayanai ko sunsuno yanayi ko kuma dauko hotunan sararin samaniya, don amfanin dan Adam. 




Yadda tauraron dan Adam ke shawagi a cikin falaki


A karon farko ana amfani ne da roket ne mai dauke da kumbo, don cilla wani tauraro zuwa sararin samaniya. Daga baya aka zo ana amfani da jiragen sama masu masifar gudu, duk da yake shi ma wannan tsari na bukatar roket wanda ke harba jirgin zuwa wani mizanin nisa cikin samaniya, kafin wannan jirgi ya ingiza tauraron cikin falaki.

Ana cikin haka sai kuma masana kimiyyar sararin samaniyar Amurka suka bullo da wata hanya wacce ta sha bamban da sauran wajen sauki da inganci. Wannan hanya kuwa ita ce ta cilla tauraron dan Adam daga babbar kumbon tashar binciken sararin samaniya da ke can sararin samaniya, wato US Space Shuttle. 

Hakan na faruwa ne domin masana na iya kera tauraron dan Adam a halin zamansu cikin wannan kumbo da ke tashar, har su harba shi. Haka idan ya lalace ko ya gama aikinsa, suna iya sanya shi cikin wani kumbo karami don aikowa da shi wannan duniya tamu don a gyara shi yadda ya kamata.

 Nan gaba, masana harkar falaki a Amurka na tunanin bullo da wani tsari mai suna Single Stage to Orbit, wato tsalle daya zuwa falaki� a misali.  


Single stage to orbit rockets


Wannan tsari zai rage yawan tashoshin da tauraron dan Adam zai bi kafin kaiwa ga falakin da aka tunkuda shi don gudanar da aikinsa. Idan har suka dace, wannan tsari zai zo ne da kumbon sararin samaniya guda daya, tafkeke, mai iya daukar taurarin dan Adam da dama, don aikawa da su zuwa cikin falakin da ya dace da su, cikin harbawa guda!

Me yasa tauraron dan Adam yake da matukar amfani?



Amfanin tauraron dan Adam bazai kididdigu ba


Kowane tauraron dan Adam yana dauke da wasu idanuwa kamar na tsuntsu wanda a turance a ke kira bird-eye view Wadannan idanuwa su kan taimakawa tauraron dan Adam domin ya iya hango abubuwa masu nisan gaske dake doron Duniya a cikin lokaci guda. 

Wannan kenan yana nuni da cewa tauraron dan Adam shine abu mafi sauki kuma mafi sauri da zai iya karbar bayanai ko aikawa da bayanai cikin kankanin lokaci kana ya yada bayanan cikin sauki wanda zai yi wuya wata na'urar dake girke a doron kasa ta iya wannan aiki.

Bayan haka kuma tauraron dan Adam yana iya ganin cikin sararin samaniya karara fiye da yadda na'urar telescope za ta yi, saboda shi tauraron dan Adam ya ketare gajimare da kuma feshin ruwa dake saman wannan duniya tamu, shi yasa nan da nan zai ya ganowa ko sunsuno sararin samaniya karara ba tare da wani abu ya kawo masa cikas ba.

Kafin zuwan kimiyyar tauraron dan Adam, maganadisun dake samar wa TV makamashi wato TV signals baya cin dogon zango saboda layin maganadisun yana tafiya ne a mike (straight line ) saboda haka dogayen gine-gine ko tsaunaka suna iya kawo tangarda, amma yanzu kuwa kimiyyar tauraron dan Adam ta magance wannan matsalar.

A da kafin zuwan kimiyyar tauraron dan Adam hanyar sadarwa da wayar salula zuwa waje mai nisa ya kan zamo tashin hankali ne babba Sakamakon rashin signals masu karfi, amma yanzu kuwa tauraron dan Adam yana karbar sakon waya da talbijin (TV) zuwa sararin samaniya a yayin da kuma zai sarrafashi sa'annan ya rarraba sakon zuwa ga inda a ke so ya isa a fadin duniya duka cikin abinda bai wuce yan dakiku ba.

Ya ya siffar tauraron dan Adam take? 


Taurarin dan Adam sunada siffofi bila'adadin

Ana kera samfurin tauraron dan Adam cikin siffofi mabanbanta da kuma fasalin girman jikinsu. Amma akwai bangarori guda biyu wadanda dole ne a samesu a kowane irin samfurin tauraron dan Adam sune; Sandar sunsuno bayanai (antenna) da kuma Ruhin jikinsa (power source).

Aikin antenna shine karbar bayanai da kuma aikasu cikin duniya ko sararin samaniya, shi kuma power source dole ne kodai ya kasance battery ko kuma inji mai aiki da hasken rana wato (solar panel). Gangar Solar engine ya kan juya sinadarin hasken rana ya zama sinadaran lantarki dake iya aiki a jikin Na'ura (electricity).

Mafi akasarin tauraron dan Adam mallakin NASA an kera shi da wasu irin gaggan kyamarori da sanso (sensor) wadanda wani lokaci suke duban duniya domin su rika karbar bayanai daga duniya suna sunsuno fasalin ruwan dake gudana a tekuna da iskar dake kadawa ko kuma fasalin muhalli, wasu lokuta kuma kyamarorin suna juyawa su rika duban sararin samaniya domin sunsuno abubuwan dake wakana cikin falaki.

Ta ya ya tauraron dan Adam yake zagaye duniya?


Yadda tauraro dan Adam ke kewaya duniya cikin falaki

Mafi akasarin tauraron dan Adam ana aika shi sararin samaniya ne a cikin kumbo (rocket). Tauraron dan Adam ya kan iya zagaye duniya ne yayinda ma'aunin gudunsa sukayi kunnen doki da adadin karfin maganadisun cikin kasa (Earth's gravity).

Idan har ba a sami wannan daidaiton ba to da tauraron dan Adam zai dinga lulukawa cikin sararin samaniya ne babu kakkautawa ko kuma ya dawo ya fado cikin wannan duniya tamu.

Tauraron dan Adam ya kan zagaye duniya a bisa ma'aunin tsayi (heights) mabanbanta da kuma mizanin karfin gudu (speeds) mabanbanta da kuma hanyoyi mabanbanta (paths).

Hanyoyi guda biyu sune sanannu wadanda mafi akasari tauraron dan Adam yake zagayewa sune "geostationary" (gee-oh-STAY-shun-air-ee) da kuma "polar."

Tauraron dan Adam mai bin hanyar geostationary ya kan yi tafiya daga yammacin duniya zuwa gabashi daura da gurun da ya ratsa duniya wato (equator). Yana tafiya ne a kusurwa daya kuma da karfin mizanin gudu daidai da yadda duniya ke juyawa.

Amma shi kuma tauraron dan Adam mai bin hanyar polar ya kan yi tafiya ne daga kusurwar kudu zuwa kusurwar arewa. Yayin da duniya ke juyawa daga kasa su kuma taurarin dan Adam sai su taskance abinda ke cikin duniya gaba daya a lokaci guda.

Shin ko taurarin dan Adam kan yi karo da junansu?



Tabbas, suna iya karo da juna. Hukumar kula da sararin samaniya (NASA) da (U.S) da kuma wasu hukumomi masana ilimin taurari sukan bi diddigin hanyoyi wadanda tauraron dan Adam ke bi a sararin samaniya. Kowane tauraron dan Adam an dasa shi ne bisa falakinsa domin kiyaye karo da juna, to amma wasu lokuta hanyoyin sukan sauya, sai dai an gano cewa yawaitar jefa taurarin dan Adam a sararin samaniya shine musabbabin abinda ke haifar da karo da juna saboda su kan yi yawa a bagire guda a cikin falaki.

A cikin Fabarairun shekarar 2009, an sami wasu taurarin dan guda biyu mallakar Amurka da Rasha sun yi karo da juna a sararin samaniya. A tarihi wannan shine karo na farko da aka samu taurarin dan Adam sun yi karo da juna bisa hatsari. 

Wane tauraron dan Adam ne aka farawa harbawa sararin samaniya? 


Tauraron dan Adam na Sputnik-1 kenan

Watakila wannan tambayar zata iya darsuwa a ranka duk sa'adda ake zancen tauraron dan Adam. To ga amsar tambayar kamar haka; Tauraron dan Adam na farko da aka fara harbawa sararin samaniya shine kirar Sputnik 1 wanda hukumar Soviet Union suka harba zuwa sararin samaniya a shekarar 1957. 

Menene tarihin tauraron dan Adam mallakar hukumar NASA?


Tauraron dan Adam na TIROS-1 kenan

Ba shakka hukumar NASA ta taka rawar gani sosai a fagen kimiyyar sararin samaniya, sun aika da daruruwan taurarin dan Adam cikin falaki, na farko shine samfurin explorer 1 wanda aka aika a shekarar 1958. Wannan tauraron dan Adam na explorer 1 mallakar Amurka, shine tauraron dan Adam na farko wanda mutum ya kera. 

Manyan na'u'rorin da aka jibge a jikin wannan tauraron dan Adam sune, na'urorin sunsuna (sensors) an sana'anta shi da nufin nadowa da kuma tattaro bayanan wani sinadarin haske dake cikin falaki mai suna cosmic rays.

Tauraron dan Adam wanda ya fara daukar hoton duniya a shekarar 1959 shine samfurin explorer 6 mallakin hukumar NASA. Sai kuma samfurin TIROS-1 a shekarar 1960.

 Duk da yake dai hotunan basu fita da kyau ba amma sun taimaka sosai wajen kara fadada ilimin binciken masana kimiyyar sararin samaniya wajen gano yadda duniya take da kuma abubuwan dake kewayenta.