Hasken Rana

Da yake Allah ya a jiye mu a tsakiyar duniya, kan wani guru da ya raba duniyar kashi biyu zuwa Arewa ko kuma Yamma, wanda masana taswirar duniya ke cewa "equator", dole ne mu hasken rana zai fi shafa fiye da sauran kasashe da ke nahiyoyin Arewa ko Kudu.

A irin wadannan kasashe namu da ke kan wannan guru, zafin yanayi kan kai maki 35 zuwa 45 a ma’aunin santigred.

Idan aka hada kuma da zafin Hamada ta Sahara da ke busowa daga Arewa, wadda ta fara cin wasu sassa na arewacin kasar nan, abin ya kan iya wuce misali.

Layin equator kenan cikin taswirar Duniya

Kasashen da suke sama ko kasan wannan guru na ekuator sun fi mu saukin jin zafin rana. A irin wadannan kasashe zafin rana baya wuce maki 30 zuwa 35 a ma’aunin na santigred.

To a wadannan ’yan shekaru kuma sai masu binciken yanayi suka gano ma yanayin namu kara dumama yake. Suka kara da cewa yawan hayakin masana’antu da na ababen hawa a birane yana yin illa ga wani shamaki a sararin samaniya da ke kare mu daga illar zafin rana.

Wannan shamaki da suka kira ozone layer yana karewa a hankali a hankali. Wasu daga cikinsu sun tabbatar da cewa rabon da a yi zafi irin na wadannan shekaru a irin kasashenmu ya kai shekaru talatin. Su kuma kasashe masu sanyi, suna samun rikicewar yanayi, daga karuwar sanyi zuwa karuwar ruwan sama wanda kan haddasa ambaliya.

Shamakin Ozone layer kewaye da Duniya, yana baiwa duniya kariya daga tsananin zafin rana.

A cewarsu, dumamar yanayi ce ke sa yanayin zafi yake ta karuwa a kasashe masu zafi kuma na sanyi yake ta karuwa a wurare masu sanyi. Yanayin zafi zai iya yin illa ga lafiya idan ya yi yawa, idan ba a dauki matakan kariya ba, kamar yadda yanayin sanyi sosai kan yi wa jiki illa idan ba a dauki matakan kariya ba. Zai iya kawo wata matsala a likitance ake kira heat stroke wato bugun rana.

A wannan yanayi maimakon jiki ya yi zafi kamar na zazzabi, an fi samun kwakwalwa ce kawai take daukar zafi, idan abin ya yi mata yawa sai ta dan dakata da aiki, shi ya sa a kan samu suma, amma da jiki ya bar zafin sai ta dawo.

Ya kamata kuma mu san cewa ba zafin rana ne kawai ke nan zai iya kawo wannan matsala ba, duk wani wuri da mutum zai shiga ya sha zafi abin zai iya karuwa.

Misali, a kan samu haka a ma’aikatan gidan buredi saboda zafin wurin ko na kamfanoni wadanda injinansu kan yawan daukar zafi.

Alamomin da mutum zai ji a yanayi na zafi sun hada da:


Madarar sinadarin hasken rana

(1) Yawan bushewar baki da makogwaro.

(2) Yawan zufa.

(3) Fitowar kurajen gumi musamman ga yara kanana.

(4) Dusashewar fata wato duhun fata.

(5) Yawan ciwon kai.

(6) Karancin fitsari ko kuma canjin kalar fitsari zuwa ruwan dorawa.

Amma idan tsananin ya yi yawa, kwakwalwa ta kasa daukar zafin yanayin, a kan samu alamu na wannan tsanani kamar haka:

👉 – Bayan ciwon kai sai a samu gigicewa.

👉 – Ba za kuma a ga zufa ba, tunda ruwan jiki ya kusa karewa.

👉 – A wasu lokutan ana iya suma musamman ma ga yara.

👉 – Baki da Lebba za su yi fari fat.

👉 – Jin muguwar kishirwa.

Hanyoyin kariya daga wannan yanayi.


Tasirin hasken rana

1. ► Yana da kyau mutum ya rika sa kaya marasa nauyi kuma masu haske ba masu duhu ba, domin kaya masu haske suna rage yawan zafin da ke shiga jiki ta fatarmu, haka kuma kaya masu duhu su kan kara wa fatarmu jin zafin rana.

Shi ya sa za a ga mutan da suna yawan sa ’yar shara fara a yanayi irin na zafi.

2. ► A guji yawo ko motsa jiki cikin rana sai dai can da yamma ko da sassafe lokacin da babu zafin rana sosai.

3. ► Idan ta kama sai an shiga rana yana da kyau mutum ya rike lema ko ya sa hula malafa wadda za ta yi masa inuwa. Mutane da yawa sun fi rike lema a yayin da ake ruwa saboda gudun bugun ruwa, amma da mutum ya san illar da zafin rana take ga jikinsa da zai rika amfani da lema a cikin rana ma.

4. ► A rika ajiyewa ko tafiya da ruwa mai sanyi a kusa domin a rika sha a kai-a kai.

5. ► Kamar kuma yadda wasu da yawa suke tambayar amfanin na’uraur sanyaya wuri, to a irin wannan yanayi a gidajenmu da wuraren ayyukanmu wannan na’ura tana matukar taimakawa kwarai da gaske wajen sanyaya wuri da jiki ma baki daya.

6. ► Idan babu irin wannan na’ura a kan samu fanka, wadda a yanzu a kan samu mai caji ko rike wuta a batir ko da ba a samun isasshiyar wutar lantarki.

7. ► A guji fita da yara unguwa ko cefane a irin wannan yanayi. A kuma lura idan an fita da su, a daina barin su a mota idan za a fita, don kada zafin mota ya buge su. Ana yawan kawo irin wadannan yaran da aka bari cikin mota suka suma asibiti a lokutan zafi.

8. ► Yana da kyau idan an shiga rana a yanayi mai zafi, da an dawo gida a watsa ruwa mai dan sanyi a jiki, don kwakwalwa ta huce.

9. ► Idan mutum yana aiki a wuri mai zafi kamar gidan biredi ko kamfani inda injina ke zafi ko wadanda ke karkashin kasa wajen hakar ma’adinai, dole yan nemi yanayi da zai saukaka zafin kamar na’urar sanyaya wuri da maka-makan tagogi da sauran dabarun sanyaya wurin.

Amfanin hasken Rana ga dan Adam


Yadda hasken rana ke amfani ga tsirrai

Haka zalika idan muka dawo ta wani bangare amfanin hasken rana yafi illarsa yawa, idan mukayi la'akari da gudummawar da hasken rana ke badawa, atakaice dai dan Adam ba zai iya rayuwa mai inganci ba ba tare da hasken rana ba kasancewar akwai sinadarai na musamman da muke samu daga hasken rana wadanda su suke taimakawa kwayoyin halittun dake cikin fatar jikunanmu wadanda suke bamu kariya da kamuwa daga cututtuka masu yawa.

Hasken rana shi yake ratsa sassan jikinmu har jini yake samun gudana, a misali da ace babu hasken rana a duniya to da jini zai daskare ne a jikinmu bazai iya gudana ba.

Yadda hasken rana ke ratsa cikin tsirrai

Bayan haka idan muka zo fannin tsirrai da bishiyoyi to lallai a wannan fagen hasken rana ke taka rawarsa kasancewar bishiyoyi da ganyaye suna karbar sinadrin chlorophyll daga hasken rana, shi yasa har kake ganin ciyawa ko ganye ya zama kore, wanda badan hasken rana ba to da ganye ko ciyawa bai zama kore ba.

Haka zalika hasken rana shi yake tallafawa tsirai su kasance cikin yanayi managarci, idan har tsiro ya rasa hasken rana to zai kasance mai rauni kuma zai kasance siriri ta yadda bazai iya amfanuwa ba kwata-kwata.

Yadda karancin hasken rana ya raunana tsirrai

A misali koda acikin gona ne kayi la'akari da shukar data ratsa ta karkashin bishiya mai inuwa zakaga yadda tsirran dake cikin inuwa suke zama a sanadiyar rashin samun ingantaccen hasken rana. Godiya ta tabbata ga Allah mahaliccin rana.

Amfanin Sinadrin Vitamin D


Amfanin hasken rana bai tsaya ga tsirrai ba ko bishiyoyi, hatta rayuwar dan Adam zata tagayyara matukar ya rasa hasken rana, haka zalika sauran dabbobi su ma suna bukatar hasken rana domin samun ingantacciyar rayuwa.

Yanzu dai ga misalin irin sinadarin da fatar dan Adam ke zukowa daga hasken rana. Wannan sinadari kuwa shine Vitamin D

Sinadarin vitamin D da ake samu daga hasken rana yana da muhammanci ga lafiyar kasusuwan mutum, amma kuma yana da amfani wajen inganta garkuwar jiki.

A wani sharhi da aka wallafa a mujallar lafiya ta Birtaniya, ya ce ya kamata a rika cin abinci mai dauke da sinadarin Vitamin D.

Sinadarin Vitamin D daga hasken rana

Garkuwar jiki na amfani da sinadarin Vitamnin D wajen samar da halittar da ke kashe kwayoyin cuta da ke haddasa rami a kwayoyin cututtuka na Bacteria da Virus.

Amma da yake ana samar da Vitamin D a fatar mutum ne a lokacin da yake rana, mutane da dama suna da karancin sinadarin a lokacin hunturu.

Gwaje-gwaje da dama da mutane suka yi wajen yin amfanin da mangunan da zai samar da sinadarin Vitamin D domin kare kansu daga kamuwa da cututtuka ya haifar da sakamako mai rudani.

Sakamakon hakan ne yasa masu binciken suka fito da kididdigar mutane 11,321 daga gwaje-gwaje daban-daban domin su samu kwakkwarar amsa.

Tawagar jami'ar Queen Mary da ke London, ta duba kwayoyin cututtuka da ke da alaka da sanyi, wadanda ke haddasa cututtuka kama daga kan mura zuwa ciwon sanyi.

Binciken ya ce mutum daya zai iya kubuta daga kwayoyin cuta a cikin ko wacce kwayar Vitamin D 33 da aka sha.

Hakan ya fi inganci a kan rigakafin mura, wanda ke bukatar sai an magance na mutum 40 domin kare mutum guda daga kamuwa da shi, duk da dai kamuwa da sanyi yafi azaba sosaifiye da murar da aka saba yi.

Mutanen da ke shan kwayar kullum ko kuma duk mako sun fi cin moriyarsa a kan wadanda suke sha duk wata da kuma ma wadannan da ma can suke da karancin sinadarin a jikinsu.

Yadda ake samar da wutar lantarki da amfani da makamashin hasken rana


Yadda hasken rana ke zama makamashin lantarki

Amfanin hasken rana ya fadada musamman a wannan karni na
Kimiyya da fasaha wani abu ne da ba yadda mutum zai rayu a ce bai amfana da shi ko ta yaya ba.

Wannan amfanin kuwa ya hada da fannoni daban daban na rayuwa kama daga abinci da mu ke ci har izuwa da magunguna da mu ke sha a asibitocinmu.

To a fannin wutan lantarki, wadda dama ya samo asali ne daga kimiyya da fasahan, yanzu an samu cigaba ta yadda ake iya mai da hasken rana zuwa wutan lantarkin da taimakon shi dai cigaban kimiyya da fasahar. Amma ya abin ya ke ne?

Babu shakka hanyar amfani da hasken rana wajen samar da wutan lantarki shi ake ta faman ya yi a gidaje da asibitoci da dai sauran gurare domin samun wutan lantarki na bukatun yau da kullum.

Shi irin wannan wutan lantarki na hasken rana ana samar da shi ne ta hanyar amfani da wani sinadari wanda ake kiransa da suna silicon.

Hakika ana amfani da silicon sau dayawa wajen hada na'uran dake samar da wutan lantarki ta hanyar hasken rana.

Faifan silicon mai zuko hasken rana

Shi wannan silicon jama'a sun san shi musamman ma wadanda suka yi karatun chemistry, akan sinadari ne wanda yana cikin rukuni na hudu, wato group 4 element.

Haka kuma duk wani element dake cikin group 4 babu shakka ana kiransa da suna "metalloid."

Silicon yana da wasu halaye tattare dashi, musamman wajen hada kayan cikin na'uran lantarki domin yana taka rawan gani.

Mota mai amfani da hasken rana

Daga lokacin da hasken Rana ya haska shi wannan sinadari mai suna silicon, to sai electrons, wato kwayoyin halittun wutan lantarki dake cikinsa, wadanda zamu iya kiransu a matsayin 'charges,' sai su fara kokarin motsi daga wuri zuwa wuri, wato suna moving from one point to another point.

Irin wannan halaye da yake dashi shine sai ake amfani dashi arufe shi da gilashi ta yadda da zaran hasken Rana ya haska wannan silicon sai charges din da suke jikinsa su fara yunkurin tafiya.

A wannan lokacin akan sanya waya wanda wutan charges din zasu bi kuma shine zai zama wutar lantarki.

Karamar tochila mai amfani da hasken rana

Gwargwadon yanayin hasken rana shine gwargwadon karfin wutan lantarki da za a iya samu daga solar. Yawanci akan yi amfani da batura wanda zasu yi caji a jikin abin solar din ta yadda idan dare yayi baturan zasu baka wuta mai karfi wanda zai isheka bukatunka.

Kada ku manta kuyi sharing ga abokanku a social media domin suma su amfana