kajin Gidan gona

Yau za mu kawo muku bayani a kan yadda ake kiwon kajin da aka fi sani da kajin gidan gona, ma’ana kajin Turawa, wato Broilers da Layers a harshen Ingilishi.

Kiwon kaji ya samu karbuwa a ‘yan shekarun nan saboda alhairin da ake samu a gudanar da shi, saukin lamarin kuma shi ne kowane bangare na al’umma na iya fadawa harkar kiwon kaji ba tare da an samu wani horo na musamman ba, abin nufi a nan shi ne za ka samu matashi mace ko namiji in dai ya yi himma to zai iya samun dukkan alhairin da ake samu a kiwon kaji.

Asalin fasahar Kajin zamani (agric)


Fasahar inganta kiwon kajin zamani ta samo asali ne ganin yadda yawan al’ummar duniya ke bunkasa, wanda kai tsaye ke nuna karuwar bukatar abinci da nama a tsakankanin jama'a.

A bangare guda kuma ta dalilin yadda ilimi ke kara habbaka da saukaka, shi ne ya sa masu ruwa-da-tsaki a harkar dabbobi kamar Malaman noma da kimiyyar halittu, da kuma Likitocin dabbobi (Animal Scientists, Agric Engineers, Animal Doctors, Genetic Engineers etc), suka zauna suka tattauna a kan yadda za’a inganta kiwon kajinmu na gida, su zama suna kwai a kowane lokaci, kuma suna saurin girma a kankanen lokaci ta yadda za’a sami isasshen kwai da nama ga al’ummar duniya.

Wannan kuwa fasahar ta fara samuwa ne a kasashen da suka cigaba musamman kasashen Turai da Amurka fiye da shekaru dari da suka wuce.

A sakamakon haka, an samu ci gaba sosai a harkar kiwon kaji da sauran tsuntsaye da ma dabbobi gaba daya.

Yanzu alkaluma sun nuna cewa, sama da kaji biliyan hamsin ake kiwatawa a duniya duk shekara.

Nijeriya kuma na sahun gaba a Afirka wajen harkar kiwon kaji da tsuntsaye.


Rabe-Raben Kajin Turawa


Za a iya kasa kajin gidan gona ta la’akari da amfaninsu kamar haka:

1. Kajin kwai ko Layers :


Layers kenan

Layers sune wadanda ake renonsu daga rana ta farko har tsawon sati 16-18 kuma sukan fara saka kwai a tsakanin sati na 16 zuwa 20.

Suna cigaba da yin kwai har shekara daya ko daya da rabi, in dai akwai kula sosai suna iya kai wa fiye da haka.

2. Kajin nama ko Broilers:


Broiler kenan

Sune Wadanda ake renonsu har tsawon sati 7, 8 ko sati 10 gwargwadon yadda mai kiwo ya bayar da dama.
A wannan lokacin ake sayar da su a kasuwa. Galibi ana kiwatasu ne don namansu.

3. Kwankwaras ko (Cockerels)


namijin cockerel kenan

Wadannan su ne mazajen layers masu kwai. Kwankwaras su ne wadanda kamfanin kyankyasa baya bukatarsu sosai, saboda da haka ake sayar da su da matukar araha, su ma suna daukar sati 16-20, kafin su girma.

Kuma sun hada da launin farare da bakake masu dishin-dishin fari ko wake-wake.

Yadda za a yi kiwon kaji ba tare da samun matsala ba


Kajin zamani suna son tsafta

Domin kiwon kaji na tattare da matsaloli da daman gaske, yawan asarar da ake tafkawa ya sa mutane da dama ke gudun shiga harkar kiwon kaji, amma wadanda suka jure matsalolin da a kan fuskanta a kiwon kaji suna bayar da labarai masu dadin ji a kan alkhairin da suke samu a harkar kiwon kaji.

Domin karfafa gwiwa ga masu hankoron fada wa kiwon kaji, mun dan tsakuro maku wasu matakai masu mahimmanci da ya kamata mai sha’awar fara kiwon kaji yakamata ya bi domin samun alkhairin da ke ciki . Matakan sun hada da:

(i) Shawarar irin kajin da kake son fara kiwo

A nan yana da matukar mahimmanci kasan wadanne irin kaji kake da sha’awar fara kiwo, kuma mene ne makasudinka na shiga harkar kiwon, kana son mai kwai ne ko domin nama ko kuma zaka yi ne domin kaci kai da iyalinka?

Sanin wadannan bayanai, yana da mahimmanci, da yawa wasu na shiga harkar kiwon kaji ne ba tare da sun san ainihin abin da suke so ba.

(ii) Zana bangaren da Kake Son ka shahara a kai

Bazai yiwu ka mamaye dukkan bangaren da ya shafi harkar kiwon kaji da muke da shi ba, akwai bukatar ka zayyana bangaren da kake son ka bayar da karfinka a kai, yin haka kuma zai taimaka sosai ya ba ka damar da zaka amfana da kuma sanin bangarori da dama da ya shafi bangaren da ka zaba.

Saboda haka bayan ka tanaji kajinka kamar yadda aka ambata a sama, daga irin tanajin da kayi zaka san irin kalar abincin da ya kamata kaba su.

Wadanda za a yi kiwonsu domin a samu kwai abincinsu daban da wanda ake bukatar nama daga gare su.

Sannan kaji na bukatar kulawa ta musamman ta hanyar tsaftace gurin kiwo da basu magunguna da wadatatccen abinci.

Shirye-shiyen fara kiwon kaji kowane iri

Kalli wannan bidiyo dake kasa zai taimaka maka sosai wajen fara kiwon kajin gidan gona cikin sauki




 A lura da kyau wannan tsarin ana yi wa kowanne kiwon kaji ko ne misali Broilers da layers da noilers da brahma da kajin gida da talotalo da sauran su.

Da farko dole kana bukatar inda za a ajiye su. DAKI KO KEJI.

In keji ne dole ya zamana an yi shi da inganci kuma wadatacce ta yadda hannunka zai kai ko’ina ba tare da matsala ba.

In daki ne ya zama yana da wadataccen hanyoyin iska ta ko'ina.

Shirye-shiyen zuwan kaji

Kafin a je a yi “booking” kaji a wajen diloli ko kamfanin samar da kaji ya kamata a tanadi wasu muhimman abubuwa…

Me za a tanada?

Wadannan abubuwan sune kamar haka:



(1) Abin shan ruwan kananan kaji (Chick drinkers)

(2) Abincin su (chick feeders)

(3) Jarida (newspapers)

(4) Fitilar kwai (lanterns) ko risho (Stove) ko gawayi (Charcoal)

(5) Kwali

(6) Kashin kafinta (wood shaving) ko garin katako ko buntun shinkafa (rice husk)

Bayan an tanadi wadannan kayan an ajiye. Sai a je a yi “booking” a wajen dilolin kaji na gaskiya kowanne irin kaji ne. Za a ba ka rasit kuma a fada maka ranar da za kaje ka dauka. Baya wuce kwana bakwai. Kwana uku ko biyu kafin zuwan kaji

A lura da kyau:

👇

Wannan gabar ita ce kashin-bayan kiwon kaji.

In aka samu matsala a wannan gabar to komai ya lalace!

Za a tanadi fitila wato joni ko duk wani abu da za a haska dakin da shi.

Da kuma Silifa wanda za a rika shiga dakin kajin da shi. Ba a shiga da takalmin da ake amfani da shi yau da kullum.

Sai safar hannu wato ta asibiti (glove)

Duk ana bukatar su a dakin kaji.

Kuma kofar dakin kajin dole ta kalli Kudu ko Arewa. Ba a so rana tana haska cikin dakin ko kejin.

Kwana uku ko biyu kafin zuwan kaji

Za a wanke dakin sosai za a yi amfani da kowanne irin maganin kwari. In an wanke za a bar dakin a bude ya sha iska sosai amma kar a bari bera da kadangaru su shiga.A

Kwana biyu ko daya kafin zuwan kaji 

wanke duk abubuwan shan ruwansu da na cin abincinsu (a kula kar a yi amfani da sabulu ko omo) a wanke abubuwan da ruwa a sa hannu kadai ya wadatar. A shanya su a rana.

Awa biyu ko daya kafin zuwan kaji

Sai a shiga dakin a buga kwalayen a gewayen dakin.



Sannan sai a zuba kashin kafintan ko abinda aka tanada. Sai a shimfida jaridar nan a cikin dakin; a tabbatar an rufe ko’ina saboda ba a so kajin suna cin diddigar katakon; za a iya likewa da koko mai siga

KARANTA WANNAN: ►  Cututtukan Dake Addabar Kaji Da Maganinsu

Daga nan sai a kawo kayayyakin reno ( brooding equipment). Kananan kaji da aka kyankyasa a ranar suna bukatar dumin da ya kai 35.5 centigrade. Shine dumin da iyayensu in sun kyankyashe za a ga suna rufe su da gashinsu don ba su wannan dumin.

Za a yi amfani da fitilar kwai guda uku shine zai ba kaji dai-dai wannan dumin. Ko a yi amfani da risho biyu shima zai yi wa kaji Dari dai-dai amma kar a bari ya yi hayaki.

Yadda ake rataye fitila ko kwan lantarki a dakin kaji

Ko wutar lantarki kwai mai 100 watt bulb guda biyu zai ba kaji Dari wannan dumin. Ko gawayi a sa shi a kasko ko wani mazubi. Da gawayi da risho za a dora su akan abu mai tudu wanda kajin ba za su tarar ba.

Haka fitilar kwai da kwan wutar lantarki za a rataye su yadda kajin ba za su tarar da shi ba.

Awa daya kafin dauko kaji

A tabbatar an sa duk abin dumama daki kuma yana aiki yadda ya kamata.

Dauko kaji: a je a dauko kaji da safe ko da Yamma kar a yarda a dauko su da rana.

Isowar kaji: In an zo da kajin sai a bude su a kwalin daga kofar dakin nasu sai a zuba ana kirga su. Da zarar an gama a yi nesa da kwalin ko ma a kone shi ya fi.

Sai a sa musu ruwan sha amma za a yi amfani da kowanne irin “anti stress” ana samun sa a kowanne shagon sayar da magungunan dabbobi.

Ko a zuba musu “Glucose D”

Ko a zuba musu siga a maimakon “anti stress” duk amfanin su daya ne.

In za a yi amfani da “Glucose D” sachet daya ya ishi lita hudu na ruwan shansu. (abin shan ruwan kananan kaji lita hudu yake ci)


Sai a zuba musu abinci in kajin broilers ne a ba su BROILERS STARTER in kuma Layers ne a zuba musu CHICK MASH.

A kula a zuba musu abinci biyu bisa uku na muzubin abincinsu (feeder)

Sai a tsaya a kalle su da kyau a ga ya yanayinsu yake.